in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taruka biyu na kasar Sin suna jawo hankalin al'ummun kasashen duniya
2018-03-07 10:53:27 cri

Ana ci gaba da gudanar da taruka biyu, wato na wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar a nan birnin Beijing, tarukan da suke jan hankalin al'ummun kasashen duniya, har wasu manyan jami'ai da masana na kasashen waje da dama ke yabawa ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin shekaru biyar da suka gabata, inda suke sa ran kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya.

A baya-bayan nan ne, Raphael Tuju, babban sakataren jam'iyya mai mulkin kasar Kenya wato jam'iyyar Jubilee, ya shaidawa wakilinmu cewa, daga sakamakon da kasar Sin ta samu, ya lura cewa, abu mafi muhimmanci yayin da wata kasa ke kokarin raya kanta shi ne, kauracewa amfani da tsarin siyasa na kasashen yamma, sannan dole ne ta yi kokarin neman wata hanyar da ta dace da yanayin da take ciki. Ya na mai cewa, "Kasar Sin tana da yawan al'umma da adadinsu ya zarce biliyan 1 da miliyan 300, ina ganin cewa, dalilin da ya sa kasar Sin take gudanar da harkokinta cikin kwanciyar hankali shi ne, amfani da tsarin siyasar da ta dace da yanayin da take ciki. Kamata ya yi kasar Kenya ta koyi fasahar da kasar Sin ta samu a wannan fannin, saboda Kenya ita ma tana da kabilu da addinai da dama, ita ma tana fuskantar kalubale kamar kasar Sin. Na ga kasar Sin ta fitar da manufofin raya kasar da suka dace da yanayin da take ciki, kuma tana mai da hankali kan al'adu da rayuwar al'ummunta, gaskiya bisa tsarin gurguzu mai halayyar musamman, kasar Sin ta samu wata hanya ta raya kanta."

Babban shehun malamin dake aiki a cibiyar nazarin batutuwan zuba jari da cinikayya tsakanin kasa da kasa ta kasar Japan Ehara Noriyoshi, ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu dimbin nasarori a cikin shekaru biyar da suka gabata. "Na lura cewa, gwamnatin kasar Sin ta samu ci gaba sosai a fannin kyautata zaman rayuwar al'ummarta. Misali a fannonin samar da aikin yi da yaki da talauci da kyautata aikin ba da ilmi, wadanda ke taka muhimmiyar rawa ga bunkasar tattalin arziki a kasar."

Ehara Noriyoshi ya kara da cewa, an yi hasashen cewa, kasar Sin za ta samu karuwar tattalin arziki da kaso 6.5 bisa dari a bana, kuma yana ganin cewa, hakan zai cimma burin da kasar ta tsara wato samun ci gaba mai inganci a maimakon samun ci gaba cikin sauri kawai.

A nasa bangaren, kwararre kan batun kasar Sin na kasar Rasha Yuru Tavrovsky shi ma ya yabawa kasar Sin saboda ci gaban da ta samu a cikin shekaru biyar da suka gabata, inda ya ce, yanzu haka tattalin arzikin kasashen duniya yana tafiyar hawainiya, amma kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri, kana rayuwar al'ummarta ya samu kyautatuwa a bayyane, har ta samu babban sakamako wajen yaki da talauci da kuma kyautata muhallin halittun masu rai da marasa rai, inda ya ce ko shakka babu, sakamakon darasi ne ga sauran kasashen duniya, yana mai cewa, "Kasar Sin ta samar da wata sabuwar hanya ga ci gaban daukacin bil adama. Yayin babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da aka gudanar a bara, babban sakataren jam'iyyar Xi Jinping ya gabatar da wani tunani game da tsarin mulkin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, ko shakka babu tunanin zai taka muhimmiyar rawa ga ci gaban kasar."

Baya ga haka, yayin da yake gabatar da rahoton aikin gwamnatin a wajen taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a ranar Litinin da ta gabata, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya fitar da burin da kasar za ta cimma wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar a shekarar 2018 da ake ciki. Game da wannan ne kuma kwararre kan harkokin kasa da kasa na kasar Jamus Michael Borchmann ya bayyana cewa, taruka biyu da ake gudanarwa bayan kammala babban taron JKS karo na 19 suna da babbar ma'ana ga ci gaban kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki yanzu, ya ce ya na mai da hankali kan tarukan matuka, kuma ya na sa ran cewa, tarukan biyu za su samu cikakkiyar nasara.

Haka zalika, daraktan cibiyar nazari kan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Mexico ta kasar Mexico Enrique Dussel, shi ma yana mai hankali kan manufofin raya kasa da za a fitar yayin tarukan biyu, musamman ma yadda za a tabbatar da tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China