in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ba ya da nufin kalubalantar wani
2018-03-07 20:00:17 cri
Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a yau Laraba cewa, hadin gwiwar da ake tsakanin bangarorin Sin da Afirka ba ya da nufin kalubalantar wani, kana duk wanda ke da niyya zai iya shiga a dama da shi a hadin gwiwar.

Kafin haka, wani babban kwamandan sojan kasar Amurka mai kula da batun yankin Afirka ya furta a jiya Talata cewa, idan kasar Sin ta karbi ikon kula da tashar jirgin ruwa mai muhimmanci ta kasar Djibouti, to, za a samu matsala, domin a dab da tashar akwai wasu na'urorin musamman da sojojin wasu kasashe suka jibge.

Yayin da Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ke amsa tambayar da manema labaru suka yi masa dangane da wannan batu, ya ce, kasar Sin na fatan ganin Amurka za ta nuna adalci yayin da take kallon ci gaban kasar Sin, da huldar hadin kai dake tsakanin Sin da Afirka.

A cewar jami'in na kasar Sin, taimakawa Afirka wanzar da zaman lafiya da samun ci gaba ya dace da muradun daukacin gamayyar kasa da kasa, kana nauyi ne dake bisa wuyan dukkan kasashen duniya. Kasar Sin na son ganin karin bangarori za su shiga a dama da su a kokarin hadin gwiwa da kasashen Afirka. Kamata ya yi a kara taimakawa kasashen Afirka, maimakon kokarin illata hadin gwiwar da nahiyar Afirka take yi da sauran kasashe don neman samun ci gaban nahiyar. Kakakin ya kara da cewa, "shin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka tana da kyau ko a'a? Dangane da wannan tambaya, kasashen Afirka da jama'ar su ne suka dace su amsa wannan tambaya."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China