in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aiki da tsarin ba kwararru daga ketare biza a duk fadin kasar Sin daga ranar 1 ga watan Maris
2018-03-02 13:34:32 cri

Hukumar kula da harkokin kwararru na kasashen ketare ta kasar Sin ta ce daga jiya, 1 ga watan Maris, kasar Sin za ta fara aiki da tsarin ba kwararru 'yan kasashen waje biza a duk fadin kasar, a kokarinta na kara himmantuwa wajen bude kofa ga kwararru 'yan kasashen ketare yadda ya kamata.

Wani jami'in hukumar ya bayyana cewa, wajibi ne hukumomin wurare daban daban na kasar, su mai da hankali kan aiwatar da wannan tsari da kuma tsara shirin aiwatar da shi.

Jami'in ya kara da cewa, bisa tsarin da aka ambata a baya, yayin zuwa kasar Sin domin yin aiki, wajibi ne a ba da takardar shaidar kwararrun ketare ga masu ilmin kimiyya da fasaha da 'yan kasuwa na kasa da kasa da kwararru na musamman da kwararru masu fasaha da dai sauransu, wadanda suka fito daga kasashen ketare, suka kuma cika sharuddan kasar Sin na samun iznin yin aiki a matsayin kwararru, kana kasar Sin na bukatar su wajen raya kanta. Har ila yau, dole ne a samar da rumbun adana bayanan da suka shafi kwararrun kasa da kasa da gwamnatin Sin ke bukata, da kuma tsarin neman samun takardar shaidar kwararrun ketare tare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China