180308-shugaban-kasar-uganda-ya-ce-hukuma-fifa-na-da-imani-kan-kasarsa-bello.m4a
|
Museveni ya yi furucin ne a fadarsa dake Entebbe a ranar Litinin, yayin da tarbi kofin kwallon kafa na duniya na hukumar FIFA a Uganda bayan da ya baro Cape Town na kasar Afirka ta kudu. A cewar shugaban, hukumar FIFA tana da imani sosai kan yadda gwamnatin kasar Uganda ke kula da harkokin wasan kwallon kafa. Wannan ne ya sa aka sanya muku cikin kasashen Afirka da za su karbi kofin na FIFA.
Ban da haka, shugaban kasar Uganda ya ce yana alfahari da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasarsa mai suna Cranes, wadda ta kusa samun izinin halartar gasar cin kofin duniya da za ta gudana a kasar Rasha a bana. A cewar shugaban, ko da yake za a bukaci wasu shekaru kafin kungiyar Cranes ta kai ga zuwa gasar cin kofin duniya, amma wata rana za su samu damar hakan. Ban da haka ya ce gwamnatin kasarsa tana kokarin raya harkar wasanni musamman ma wasan kwallo kafa.(Bello Wang)