Karamin ministan harkokin kasa da kasa na kasar Uganda Henry Oryem Okello ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa,mahukuntan Uganda ba su cimma wata yarjejeniya da Isra'ila game da karbar masu neman mafaka sama da 35,000 galibinsu 'yan kasashen Eritrea da Sudan ba.
A makon da ya gabata ne dai mahukuntan Isra'ila suka baiwa 'yan Afirka dake neman mafaka da suka gujewa yaki da musgunawa wa'adin kwanaki 90 kan su bar kasar su koma kasarsu ta asali ko su nufi wata kasa ta dabam, ko kuma su fuskanci zaman gidan sarka, ba tare da bayyana sunan wata kasa ba.
Rahotanni na cewa, an baiwa 'yan gudun hijirar zabin ko dai su koma kasashensu na asali ko kuma a tusa keyarsu zuwa kasashen Uganda ko Rwanda.(Ibrahim)