in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardar MDD ya kaddamar da dakon zuwan ranar zaman lafiya ta kasa da kasa
2017-06-15 13:44:19 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya kaddamar da dakon zuwan ranar wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa, ranar da ke tafe nan da kwanaki 100 masu zuwa.

Yayin da yake tsakoci game da ranar a jiya Laraba, Mr. Guterres ya yi kira ga al'ummar duniya, da gwamnatocin kasashe, da sauran jagororin jama'a da su baiwa kudurorin zaman lafiya kulawa.

Guterres ya ce, ko da a watan Janairun da ya gabata ma, yayin da ya kama aiki a matsayin babban magatakardar MDD, ya yi makamancin wannan kira na rungumar zaman lafiya. Ya ce, ranar zaman lafiya ta duniya da ake bikin ta a ranar 21 ga watan Satumbar ko wace shekara, na da nufin cimma burin duniya, na dakile mummunan tasirin da tashe tashen hankula ke haifarwa.

Babban jami'in na MDD ya ce, batun wanzar da zaman lafiya ya wuce ajiye makamai kawai, a cewar sa buri ne da ya kunshi sulhunta al'umma, da dakile wariya tsakanin al'umma, tare da martaba hakkokin bil'adama.

Hakan ne ma ya sanya taken taron na bana zai kasance "Hadin gwiwa domin zaman lafiya: Martaba juna, tsaro da girmama kowa". Zai kuma maida hankali ga nazartar hanyoyin tallafawa 'yan gudun hijira, da 'yan ci rani a dukkanin sassan duniya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China