Sanarwar da gwamnatin birnin ta fitar, ta ce za a yi aikin gyara gidaje 236 da suka mamaye kadada 13, 430 a bana. Ta kara da cewa, wasu iyalai 15,300 ko kuma kaso 65 na wadanda za su ci gajiyar gidajen na zaune ne a gundumomi 6 na bayan gari.
Manufar aikin yi wa gidajen kwaskwarima ita ce, daukaka daraja da ingancin rayuwar mazaunan.
Gyaran gidajen da suka lalace na ci gaba da zama muhimmin batu ga gwamnati a shekarun baya-bayan nan. Kididdigar da hukumomi suka yi ta nuna cewa, ko a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta sake gina gidaje miliyan 6 ga mazaunansu. (Fa'iza Mustapha)