in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Beijing za ta kara rage adadin motocin dake neman rijista
2017-12-15 20:57:42 cri

Mahukuntan birnin Beijing sun bayyana cewa, daga shekara mai zuwa, za a kara rage yawan sabbin motocin dake neman rijista

Bayanai na nuna cewa, a halin yanzu ana warewa birnin Beijing lambobin sabbin motoci 150,000 a ko wace shekara, kuma a shekarar 2018 za a rage wannan adadi zuwa 100,000

Mazauna birnin na neman takardar neman rijistar motoci ne ta hanyar canki-canki, an dai dauki wannan mataki ne da nufin rage gurbatar muhalli da kuma cunkuson ababan hawa a babban birnin na kasar Sin.

An bullo da wannan tsari ne a shekarar 2011.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China