Jami'an ma'aikatar masana'antu da yada labarai ta kasar Sin MIIT, sun tabbatar da cewa, akwai wakilai daga jami'o'i, da cibiyoyin bincike, da kamfanoni da za su halarci taron, inda zasu tattauna game da irin damammakin da ake da su a fannin kera mutun-mutumi.
Kasar Sin ta kasance kasa mafi girma a duniya dake samar da kamfanonin kera mutun-mutumi cikin shekaru 3, lamarin da ya ba ta damar samar da kashi 25 cikin 100 na adadin mutun-mutumi na duniya baki daya.(Ahmad Fagam)