Ofishin gudanarwar shugabancin jam'iyyar ta NCP ya sanar da daukar wannan mataki ne bayan wata doguwar ganawa da ya yi a ranar Laraba, wanda shugaban kasar kuma shugaban jam'iyyar NCP mai mulki Omar al-Bashir ya jagoranta.
Al Bashir ya fadawa 'yan jaridu cewa, "shugabancin jam'iyyar yana bayyana godiyarsa ga Injiniya Ibrahim Mahmoud Hamid, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar NCP, kuma an maye gurbinsa da Faisal Hassan Ibrahim".
Wannan dan takaitaccen sauyi da aka samu a tsarin shugabancin jam'iyyar mai mulki ana sa ran zai haifar da yin garambawul a majalisar ministocin kasar a nan gaba, da suka hada da sauye sauyen mukamai a ma'aikatun gwamnatin kasar.(Ahmad Fagam)