in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da zaman taron farko na majalisar CPPCC
2018-03-03 16:53:24 cri

Da yammacin yau Asabar a nan birnin Beijing, aka kaddamar da zaman farko na taron kwamitin majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 13. Shugaban majalisar, Mista Yu Zhengsheng ya gabatar da rahoton aiki, inda ya ce, ya kamata majalisar CPPCC ta aiwatar da manufofin babban taron wakilai karo na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka yi a bara. kana, 'yan majalisar CPPCC su sauke nauyin dake kansu, ciki har da bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, da sa ido kan harkokin kasa bisa tafarkin demokuradiyya, da kuma shiga cikin harkokin siyasar kasa, ta yadda za su bayar da karin gudummawa ga raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi, da kuma raya kasar Sin mai tsarin gurguzu na zamani.(Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China