Hakan dai na kunshe ne cikin kudurin da majalissar ta cimma yayin taron zaunannen kwamitinta da ya gudana a Talatar nan. An cimma matsaya game da hakan ne bayan kada kuri'u tsakanin mambobin zaunannen kwamitin majalissar a ranekun litinin da kuma Talatar nan.
Majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin ko NPC a takaice, ita ce majalissa mafi girma bisa kundin tsarin mulkin kasar Sin, wadda a karkashin ta al'ummar kasar ke kare ikon su na gudanar da harkokin kasar. Ana kuma zaben wakilan ta bisa wa'adi na shekaru biyar biyar, kana zaunannen kwamitin majalisar ya kan kira taron shekara shekara na majalisar.