Mr Powell ya kara da cewa, ana kokarin magance dalilan dake kawo illa ga kasuwar samar da masu aikin yi a kasar da suka hada da raguwar yawan masu kwadago da shekarunsu na haihuwa ya kai 25 zuwa 54 idan aka kwatanta da lokutan baya kafin rikicin hada-hadar kudi, da kuma rashin ganin alamar karuwar albashi cikin sauri.
Har ila yau, Powell ya bayyana cewa, kyautatuwar kasuwar samar da aikin yi ba za ta haddasa hauhawar farashi a kasar ba. (Zainab)