in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Amurka ya gana da babban jami'in kasar Sin
2018-02-10 12:56:38 cri
A jiya Jumma'a, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin mista Yang Jiechi wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar ta Amurka, a fadar shugabancin kasar Amurka ta White House, dake birnin Washington, fadar mulkin kasar.

Yayin ganawar tasu, mista Yang ya waiwayi ziyarar da shugaba Donald Trump ya yi a kasar Sin a watan Nuwamban shekarar data gabata, inda ya ce shugaban Amurka ya cimma ra'ayi daya tare da shugaban kasar Sin Xi Jinping, cewa kasar Sin da kasar Amurka suna da moriyar bai daya, da nauyin dake bisa wuyansu, a kokarin tabbatar da samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da walwala a duk duniya. Kana huldar dake tsakanin kasashen 2 zata yi tasiri ga yanayin siyasar duniya. Ganin haka ya sa mista Yang ya bayyana burinsa na ganin bangarorin Sin da Amurka sun cigaba da kokarin aiki tare, da kara kokarin mu'amala da musayar ra'ayi tsakaninsu, da gudanar da wasu tarurrukan musayar ra'ayi tsakanin manyan kusoshin kasashen 2 wadanda ake saran gudanarwa a bana lami lafiya, da habaka hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da aikin soja, da harkar shari'a, da dakile fataucin miyagun kwayoyi, da al'adu, da dai makamantansu, da kokarin daidaita sabanin ra'ayi don kara karfafa dankon zumunci dake tsakanin kasashen 2.

A nasa bangaren, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, huldar dake tsakanin Amurka da Sin nada muhimmanci matuka, saboda haka ya ce akwai bukatar aiwatar da daidaiton da ya cimma tare da shugaban kasar Sin mista Xi Jinping yayin da suka yi ganawa a birnin Beijing na kasar Sin a bara. A cewarsa, kasar Amurka na son hadin kai tare da kasar Sin, don kara kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China