Kwamandan dakarun tsaro, Maj.-Gen. Lucky Irabor, ya fada a Abuja, babban birnin Najeriya cewa, ya zama tilas mambobi kasashe na tafkin Chadi su kara himma wajen yakar 'yan tada kayar bayan wadanda suka kasance makiyan kasashen. Ya bayyana hakan ne a lokacin taron kasa da kasa da aka shirya game da tafkin Chadi, da nufin sanar da duniya kan irin dunbun tattalin arziki dake yankin, da kuma kalubalolin dake addabar tafkin wanda ke fuskantar barazanar kafewar. (Ahmad Fagam)