in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 186 cikin wata guda
2018-02-15 11:54:20 cri

Kwamandan sojojin Najeriya mai yaki da mayakan Boko Haram a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar Rogers Nicholas, ya bayyana cewa, dakarunsa sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 186 cikin wata guda kacal, a yakin da suke yi na kawar da 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabashin kasar da ma yankin tafkin Chadi.

Rogers wanda ya bayyana hakan jiya Laraba, ya ce matakan da sojojin ke dauka ya haifar da kyakkyawan sakamako tare da karya lagon kungiyar. Haka kuma dakarun sun yi nasarar lalata tare da kwace sansanin nan na "Camp Ziro" da mayakan ke amfani da shi a dajin Sambisa, baya ga sama da mayakan na Boko Haram 1,000 da suka mika wuya ko aka kama sakamakon wannan mataki.

A ranar Talata ne dai shugaban Najeriya muhammadu Buhari ya ce, an kusa kawo karshen kungiyar a Najeriya, ganin yadda ba ta samun karin magoya baya dake shiganta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China