in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya ce Boko Haram na fuskantar karancin mabiya
2018-02-14 10:56:24 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayin da kungiyar 'yan ta'addar Boko Haram ke samun koma baya wajen daukar masu yi mata hidama, sannu a hankali zamanin ayyukan ta'addanci na gab da zuwa karshe a kasar ta yammacin Afrika.

Shugaba Buhari, a yayin da yake karbar wasikun nuna jinjina daga wasu jami'an diplomasiyya a Abuja, yace, tun lokacin da aka kaddamar da sabon salon yakin da mayakan, kungiyar 'yan ta'addan ta fara fuskantar matsin lamba na rashin samun damar daukar karin sabbin mayakanta aiki.

Shugaban na Najeriya yace, kungiyar 'yan ta'addan ta rasa karfin ikon da take dashi a lokutan baya, inda a da ta kwace iko da wasu yankunan kasar, hakan ne ma ya sanya kungiyar ta buge da kaddamar da hare haren kunar bakin wake a tsakanin alummomin kasar, amma sannu a hankali za'a ga bayan kungiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China