in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta tona rijiyar burtsatsai a tungar kungiyar Boko Haram dake dajin Sambisa
2018-02-17 12:33:13 cri
Dakarun gwamnatin Nijeriya dake yaki da mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, sun tona rijiyar burtsatsai a maboyar 'yan ta'addan dake dajin Sambisa.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Nijeriya Sani Kukasheka ya fitar, ta ce rijiyar kari ne akan ayyukan gyaran tituna da ake yi domin samar da kayayyakin more rayuwa a dajin da ma al'ummomin yankin.

Sani Kukasheka ya ce an tona rijiyar ne domin samar da ruwa ga dakarun da sauran al'ummomin yankin, a wani yunkuri na kyautata yanayin rayuwa a dajin

A cewarsa, aikin wani bangare ne na kakkabe ragowar mayakan Boko Haram.

Sani Kukasheka ya kara da cewa, rundunar ta tona rijiyar ne a sansanin 'yan ta'addan na Sabil Huda dake dajin bayan ta fatattake su, domin samar da ruwan sha mai tsafta ga dakarunta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China