in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon bayan matakan Pakistan na yaki da ta'addanci
2018-02-27 19:54:03 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan matakan da kasar Pakistan ke dauka game da yaki da ayyukan ta'addanci, sannan ta yi kira ga kasashen duniya da su nazarci matakan kasar na yaki da ta'addanci bisa adalci. Lu Kang wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin taron manema labarai, ya ce gwamnati da al'ummar Pakistan sun sadaukar da kansu tare da ba da gudummawa matuka a yakin da mahukuntan kasar ke yi da ayyukan ta'addanci. Haka kuma kasar ta yi kokari sosai a hare-haren da take kaiwa ta kasa da ma yadda take yakar matsalar ta bangaren kudi. (Ibrahim)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China