in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya yi allah wadai da harin da aka kai Pakistan
2017-12-19 11:09:40 cri
Babban magatakardan MDD Antonio Gutarres ya fidda wata sanarwa a jiya, inda ya yi allah wadai da harin ta'addanci da aka kai lardin Balochistan na kasar Pakistan a ranar 17 ga wata.

Cikin sanarwar, Mr Gutarres ya yi allah wadai da kakkausar murya kan harin da aka kai a wata majami'a dake birnin Quetta na lardin Balochistan, kana ya nuna juyayi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Bugu da kari, ya ce, ya kamata a gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi a gaban kuliya.

A ranar 17 ga wata ne, aka kai hari kan wata majami'a dake birnin Quetta na lardin Balochistan a kudu maso yammacin kasar Pakistan, inda aka yi mumunan musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da maharan, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla 8, yayin da wasu fiye da 10 suka jikkata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China