in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pakistan: Yawan mutanen da suka mutu sakamakon gobarar tarkar mai ya karu zuwa 158
2017-06-28 13:57:29 cri

A jiya Talata 27 ga wata ne asibitin yankin Bahawalpur dake jihar Punjab a gabashin kasar Pakistan, ya tabbatar da cewa, ya zuwa yanzu a kalla mutane 158 ne suka rasu, sakamakon gobarar da ta kama wata motar dakon mai a ranar 25 ga wata, sa'an nan wadanda suka jikkata sun kai 111, kuma suna samun jinya a asibitin, a ciki hadda 22 dake cikin halin gaggawa, don haka kila yawan masu rasa rayukan na su zai iya karuwa.

Ya zuwa yanzu dai, ana bin basahin dalilin da ya haddasa gobarar. Kuma bisa binciken da 'yan sanda suka yi, an ce, kila gobarar ta abku ne sakamakon taba da jama'a masu kallo suka jefar.

Shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain da firaministan kasar Nawaz Sharif, sun nuna bakin cikinsu game da aukuwar hadarin, tare da bukatar hukumomin da abin ya shafa su gudanar da aikin ceto cikin hanzari. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China