A cewar ma'aikatar, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka cikin shekaru 5 da suka wuce, sun hada da rufe wasu tsoffin masana'antu masu yin amfani da tsoffin fasahohi, da kara yin amfani da makamashi mai tsabta, da rage kona makamashin kwal, da gyaran fuska a fannonin da suka shafi ayyukan samar da wasu sinadaran da ka iya gurbata muhalli, gami da kyautata tsarin sa ido kan ingancin iska.
Ma'aikatar kiyaye mutalli ta kasar Sin ta kara da cewa, har yanzu ana fama da matsala mai tsanani ta gurbacewar iska a wasu wuraren kasar, da wasu lokuta, don haka ana shirin tsara wata manufar ta shekaru 3 don tabbatar da kara tsabtace iska a kasar.(Bello Wang)