in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi odar manyan jiragen sama kirar kasar Sin samfurin C919 guda 815
2018-02-26 13:45:08 cri
A yau Litinin, wani kamfanin kasar Sin mai taken Huarong ya kulla yarjejeniya da kamfanin COMAC mai samar da jiragen sama na kasar Sin, a birnin Beijing, don tabbatar da niyyar sayen babban jirgin saman fasinjar samfurin C919 guda 30, da jirgin sama mai jigilar fasinjoji samfurin ARJ21 guda 20. Bisa sabuwar yarjejeniyar da aka kulla, kamfanonin kasar Sin da na ketare da suka nemi sayen jirgin saman C919 sun kai 28, kana yawan jiragen da aka yi odar ya kai 815.

An ce, jirgin saman samfurin ARJ21 ya riga ya fara aiki a wurare daban daban, kana yawan fasinjojin da irin wannan jirgin sama ya dauka ya kai fiye da dubu 49. Kana babban jirgin sama na C919 shi ma ya fara aiki. Sa'an nan ana kokarin kirkiro wani sabon nau'in babban jirgin sama samfurin CR929 a kasar Sin. Zuwa yanzu masu neman sayen jirgin saman na ARJ21 sun kai kamfanoni 21, yayin da yawan jiragen da suke bukata ya kai guda 453.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China