A cewar jami'in kasar ta Sin, ana ta kokarin samar da hidimar inshora ga karin al'ummar kasar Sin, kana irin hidimar da ake samarwa na kara samun kyautatuwa. Ya zuwa yanzu, ana ta daga kudin tallafin da ake baiwa tsoffi cikin shekaru 13 a jere, lamarin da ya amfanawa ma'aikatan da suka yi ritaya daga aiki fiye da miliyan 100.
A sa'i daya kuma, gwamnati ta kara baiwa tallafin kudin ganin likita ga jama'ar kasar, kana idan wani ya kamu da cuta mai tsanani, to, kashi 80% na kudin da yake bukata wajen ganin likita zai iya samun sa ta inshorar lafiyar. (Bello Wang)