Lavrov ya bayyana haka ne a yayin da yake ba da amsa kan tambayoyin 'yan jaridar kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin, a yayin taron manema labaru da aka shirya jiya Litinin game da ayyukan diflomasiyyar Rasha a shekarar 2017, inda ya nuna cewa, kasashen Rasha da Sin sun tsara taswirar warware matsalar zirin Koriya, kana za su ci gaba da goyon bayan gudanar da shawarwari kai tsaye a tsakanin bangarorin da batun ya shafa. Game da batun Syria kuwa, ministan ya ce kasashen Rasha da Sin suna tsayawa tsayin dak na ganin an warware matsalar a siyasance ta hanyar martaba kudurorin MDD da batun ya shafa. A ganinsu, kamata ya yi a shigar da dakarun dake adawa da gwamnatin kasar cikin shawarwarin siyasar, ta yadda za a samu wakilcin kowane bangare. (Bilkisu)