A wajen taron da aka yi a jiya Asabar, an saurari ra'ayoyin jama'a dangane da kudurin kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kan zurfafa yin kwaskwarima ga hukumomin jam'iyyar gami da na kasa baki daya. Za'a kuma gabatar da gyararren kudurin ga cikakken zaman taro karo na uku na kwamitin tsakiya karo na 19 na jam'iyyar Kwaminis ta Sin don a duba shi.
Har wa yau, taron ya yi nuni da cewa, tun da aka kira babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 ya zuwa yanzu, kwamitin tsakiya na jam'iyyar dake karkashin jagorancin Xi Jinping ya nuna cewa, babban buri na zurfafa yin gyare-gyare daga dukkanin fannoni shi ne, kyautatawa gami da raya tsarin gurgurzu mai sigar musamman ta kasar Sin, da kara zamanantar da tsarin tafiyar da harkokin mulkin kasa. Don haka kamata ya yi a yi kokarin warware matsalolin da suka jibinci tsarin hukumomin jam'iyyar Kwaminis gami da na kasa baki daya, ta yadda tsarin gurguzu na kasar Sin zai kara taka rawar a-zo-a-gani.(Murtala Zhang)