Ga misali, a wani wuri mai ni'ima da ake kira dutsen Qing-cheng-shan dake lardin Si'chuan na kasar Sin, an kafa wasu ban daki na zamani musamman ma domin biyan bukatun iyalai, wato iyaye da yara, wadanda suke yawon shakatawa a wajen. A cikin wadannan bayan gida na zamani ake samun na'urorin da yara za su iya amfani da su, da na'urorin ba da sauki ga nakasassu, da madannin da za a iya danna don kirawo mutane idan akwai bukatar gaggawa, da dai sauran na'urorin zamani iri-iri.
An ce, tun da hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin ta kaddamar da shirin gina karin ban daki a shekarar 2015, har zuwa karshen shekarar 2017, kasar Sin ta riga ta gina da kuma gyaran fuskar wasu ban daki da yawansu ya kai dubu 70. Ban da haka kuma, ana da shirin kara gina wasu dubu 24 a shekarar 2018, kana a shekaru 3 masu zuwa za a kammala shirin gina ban daki dubu 64 a wuraren shakatawa.(Bello Wang)