Shugaban Bongo ya yi rangadi a cikin jirgin ruwan na kasar Sin, inda ya ganewa idonsa yadda ake kokarin jinyar jama'ar Gabon da suke da bukata, ya kuma gana da wadanda suke kwance a cikin jirgin wadanda aka yi musu tiyata. Ban da haka kuma, shugaban ya duba faretin girmamawa da sojojin ruwan kasar Sin suka yi, ya kuma shiga cikin jirgin sama mai saukar ungulu na aikin ceto, tare da sauraron bayanan da aka yi masa dangane da jirgin ruwan mai kula da aikin jinya.
Lokacin da shugaba Bongo ya ambaci huldar dake tsakanin kasarsa da Sin, ya ce burinsa shi ne a karfafa zumunta da hadin gwiwa da ke akwai a tsakanin kasashen 2. A cewarsa, kasar Sin abokiyar Gabon ce, yayin da Gabon ita ce aminiyar kasar Sin, zumuncin dake tsakaninsu yana da zurfi, kuma yana da tarihi. Yadda aka tura jirgin ruwan na aikin jinya don ya tafi kasar Gabon ya karfafa huldar dake tsakanin bangarorin 2, kana ya aza tubali ga kyautatar huldar a nan gaba.
Jirin ruwan musamman mai kula da aikin jinya na kasar Sin na "Peace Ark" ya isa kasar Gabon a ranar 1 ga watan da muke ciki. Zuwa ranar 7 ga wata, an riga an yi jinyar jama'ar Gabon kimanin 6092.(Bello Wang)