in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin ruwan dake aikin kiwon lafiya na kasar Sin ya kai ziyara kasar Gabon
2017-10-02 13:03:17 cri
A jiya Lahadi 1 ga watan Oktoban nan ne, babban jirgi dake bada hidimar kiwon lafiya, na rundunar sojan ruwan kasar Sin, wanda a yanzu haka yake gudanar da aikin da aka yiwa lakabi da "Mission Harmony 2017", ya isa mashigin teku na Owendo dake kasar Gabon.

Jirgin ya fara wata ziyarar sada zumunta ne ta tsawon yini takwas a kasar, gami da bayar da hidimar kiwon lafiya ga al'ummar wurin. Wannan shi ne karon farko da jirgin ruwan sojan kasar ta Sin ya ziyarci kasar ta Gabon.

Jirgin ruwan sojan kasar ta Sin zai gudanar da aikin jinya ga mutanen da suke da bukata, tare kuma da tura wasu rukunonin masu aikin jinya da dama zuwa asibitocin Gabon daban-daban domin gudanar da ayyukan kiwon lafiya.

Har wa yau, jirgin ruwan zai tura wasu rukunoni, don gyaran na'urorin dake cibiyoyin kiwon lafiyar kasar, yayin da rukunonin masu aikin kiwon lafiya da al'adu, za su gudanar da ayyukan sada zumunta a sansanin soja, gami da wasu makarantun firamare na kasar ta Gabon. Dadin dadawa, jami'an wannan jirgin ruwan soji na kasar Sin, za su shirya wata liyafa, da gasar wasan kwallon kafa da za a yi tsakanin su da takwarorinsu na kasar ta Gabon don karfafa zumunci.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China