Huawei da Xiaomi, su ne kadai kamfanoni da suka samu bunkasar ciniki ba tare da tangarda ba, inda kamfanin Huawei ya kai kaso 7.6 yayin da na Xiomi ya kai kaso 7.9.
Cinikin wayar hannu a duniya ya kai kusan maki miliyan 408 cikin rubu'i na a karshe na bara, adadin da ya ragu da kaso 5.6 a kan na makancin lokacin a shekarar 2016.
Wannan shi ne karon farko da aka samu raguwar cinikin wayar hannu tun daga shekarar 2004, da kamfanbin Gartner ya fara bibiyar kasuwar wayar hannu ta duniya. (Fa'iza Mustapha)