in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa miliyan 386 ne suka yi bulaguro yayin hutun bikin bazara
2018-02-22 10:28:21 cri

Hukumar kula da yawon shakatawa ta kasar Sin, ta sanar a jiya Laraba cewa, wurare masu ni'ima na kasar sun samu bakuncin masu yawon shakatawa da yawansu ya kai miliyan 386 a lokacin hutun bikin bazara, wato wata sallar gargajiya ta kasar Sin, inda a wannan karo yawan mutanen ya karu da kaso 12.1 bisa na shekarar bara.

An ce wuraren da suka fi jan hankalin masu yawon shakatawar sun hada da yankunan karkara da kauyuka masu ban sha'awa da dai sauransu. Kana kimanin kashi 50 daga cikin masu yawon shakatawar sun yi bulaguro ne ta hanyar tuka motoci da kansu.

Ban da haka kuma, wuraren da Sinawa suka ziyarta yayin hutun bikin bazara sun hada da kasashe da yankuna 68 na duniya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China