in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta fara sayar da kadarorin da aka kwato
2018-02-20 11:38:42 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fara sayar da kadarorin da ta kwato wadanda suka hada da filaye da gidaje kuma har yanzu babu wanda ya fito ya yi ikirarin nasa ne.

Shugaban wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, ya ce za a zuba kudaden kadarorin da aka sayar cikin baitul-malin gwamnati ganin yadda aka haramtawa da dama daga cikin mutanen taba kadadorin da suka sata.

A cewarsa, ba abin mamaki ba ne yadda adadin wadannan ba sa fitowa fili su nuna mallakar wadannan kadarori ke karuwa, bayan da hukumar dake yaki da cin hanci ta gano irin wadannan kadarori, saboda gwamnati tana bin hanyoyin da doka ta tanada wajen kwato kadarorin da aka sata.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka dai Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka ta dauki matakan yaki da matsalar cin hanci da rashawa, musamman a bangaren gwamnati, inda take amfani da matakan dakatar da matsalar da kwato kadarori a matsayin hanyoyin da ta mayar da hankali a kai da sauransu.

Gwamnatin Najeriyar dai ta yi alkawarin kara inganta manufofinta na yaki da matsalar cin hanci da rashawa a kasar, tana mai cewa, hakan ya taimaka matuka ga nasarorin da ta samu a yakin da take yi da cin hanci da rashawa da kudaden da aka bankado. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China