in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani kwararre a Najeriya ya ce bikin bazarar Sinawa yana kara samun karbuwa a Afrika
2018-02-17 12:22:16 cri

Wani kwararre a fannin huldar kasar Sin da kasashen Afrika ya ce bikin bazarar Sinawa ya yi matukar samun tagomashi a Afrika a wannan shekara, kuna yana kara samun karbuwa, kana wata alama ce dake nuna yadda ake kara samun cudanyar al'adun kasar Sin da kasashen Afrika.

A wata hira da ya yi kwanan nan, Charles Onunaiju, daraktan cibiyar nazarin al'amuran kasar Sin a Najeriya dake Abuja babban birnin kasar, ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, irin kyautattun bukukuwan da aka gudanar tun gabanin fara bikin bazarar Sinawa a duk fadin Afrika tamkar hujja ce dake nuna yadda ake samun karin kyautatuwar dangantaka tsakanin Sin da Afrika.

A ranar Jumma'a al'ummar Sinawa a duk fadin duniya suka gudanar da bikin murnar sabuwar shekarar kare bisa kalandar gargajiyar kasar.

A ranar Lahadin makon jiya, al'ummar Sinawa dake tarayyar Najeriya suka gudunar da shagulgulan bikin murnar sabuwar shekarar 2018 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wanda aka gudanar a Abuja.

Bikin, wanda ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya ya shirya, ya samu halartar dubun sinawa, da jami'an gwamnatin Najeriya da sauran jama'ar dake sha'awar fahimtar al'adun Sinawa.

Onunaiju ya ce, kare alama ce ta biyayya da nacewa, don haka ana fatan a wannan shekarar ta kare matsayin dangantakar Sin da Afrika za ta kai wani sabon mataki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China