Salame, wanda kuma shi ne wakilin musamman na sakatare janar na MDD, ya bayyana hakan ne bayan wani taron ganawa da wakilan siyasa da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro na kudancin Libya inda suka tattauna game da batun matsalolio dake addabar biranensu, musamman matsalar tabarbarewar tsaro a kan iyakokinsu.
Salame ya fadawa taron 'yan jaridu a Tripoli cewa, dole ne a magance matsalar yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba a kasar, ya kara da cewa ba'a sanya ido a kan iyakokin kasar kuma babu wani tsarin bai daya na hukumomin kasar Libya dake hana bazuwar makamai.
A cewarsa MDD tana aiki tukuru kuma tana tuntubar kasashen duniya masu yawa don hana shigar da makamai cikin kasar ta Libya.
Sai dai wannan jami'in MDDr bai ayyana kasashen da yake tattaunawa da su wajen hana shigar da makamai cikin kasar Libyan ba. (Ahmad)