in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya jaddada bukatar bunkasa tattalin arzikin da zai samar da kayayyaki da hidima
2018-02-14 10:15:22 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar ya jaddada bukatar ganin an bunkasa tattalin arzikin da zai rika samar da kayayyaki masu inganci da kuma hidimomi. Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci yankin kudu maso yammacin kasar, gabanin bikin bazara na al'ummar Sinawa.

Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya kuma ziyarci kamfanin samar da kayayyakin laturoni dake Chengdu, babban birnin lardin Sichuan, inda ya kalli yadda ake samar da farentan dake nuna fuskar wayoyin salula, daga bisani kuma aka yi masa bayani game da matakan tsaron kayayyakin da kamfanin ke samarwa.

Shugaba Xi ya yi kira ga kamfanoni, da su kara kokari a fanin kirkire-kirkire ta yadda za su yi gogayya a kasuwannin duniya. Ya kuma jaddada cewa, akwai bukatar kamfanoni su karkata daga kayayyaki kirar kasar Sin zuwa wadanda aka kirkiro a kasar, su kuma mayar da hankali ga batun inganci maimakon samar da kayayyaki barkatai cikin hanzari. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China