Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon taya murnar bikin bazara na al'ummar Sinawa ga jami'an jam'iyyun da ba na kwaminis ba, da kungiyar cinikayya da masana'antu ta kasar Sin ko ACFIC, da kuma sauran jama'ar kasar.
Shugaba Xi wanda shi ne kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana jagoran kwamitin koli na hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin wani taro da ya gudana a nan birnin Beijing.
Shugaban na Sin ya kuma yi kira ga 'yan jam'iyyun da ba na kwaminis ba, da sauran al'ummar kasar da su yi hadin gwiwa da JKS wajen raya tsarin mulkin gurguzu mai halayya ta musamman ta kasar Sin.
Ya ce, yayin da tsarin mulki na gurguzu da kasar Sin ke gudanarwa ke shiga sabon zamani, ya dace tsarin jam'iyyu sama da daya ya sauya salo, don haka akwai bukatar daidaita tafiya tsakanin sauran jam'iyyu da JKS, ko a kai ga cimma nasarorin da aka sanya gaba.
Shugaba Xi ya kara da cewa, a shekarar 2017 kasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin ci gaban ayyukan jam'iyya da kasa baki daya, don haka ya zama wajibi sauran jam'iyyu, da al'uumar kasa su kara ba da hadin kai ga gwamnatin tsakiya da jagorancin kwamitin koli na JKS.
A yayin taron da ya gabata, jagorori daga jami'iyyun da ba na kwaminis ba, da ACFIC sun gabatar da bayanan ayyukan su, da ma wadanda suke fatan gudanarwa a nan gaba.(Saminu)