in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya amince da bada rancen dala miliyan 200 domin tallafawa bangaren noma a Nijeriya
2017-03-25 12:51:23 cri

Bankin duniya ya amince da bada rancen dala miliyan 200 domin kara tallafawa Nijeriya, a kokarin da take na inganta ayyukan kananan da matsakaitan manoma.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Daraktan Bankin a Nijeriya Rachid Benmessaoud, ya ce an bada rancen ne la'akari da rawar da bangaren harkokin noma ke takawa wajen fadadawa da kuma bunkasa tattalin arziki cikin lokaci mai tsawo.

Rachid Benmessaoud ya ce hukumar raya kasashe ta bankin IDA ce ta bada rancen mai kudin ruwa kalilan.

A cewarsa, an bada rancen ne karkashin ka'idojin hukumar IDA, sannan za a biya cikin shekaru 25 da karin wasu shekaru 5.

Daraktan ya ce rancen zai mai da hankali ne ga muhimman bangarorin noma kamar karancin samun albarkatun gona da rashin kudin samar da cibiyoyin sarrafa kayayyakin gona, da kuma rashin kayayyakin aiki.

Haka zalika, zai kuma mai da hankali ga matsaloli karancin amfani da fasahar zamani da na karancin samun damar kai kayayyakin gona kasuwa.

Benmessaoud ya kara da cewa manoma mata da matasa a fannonin kiwon dabbobin gida da na hallitun ruwa da kuma na tssirrai ne za su ci gajiyar shirin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China