A yayin ganawar, Wang Yong ya bayyana cewa, Sin tana dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka, kana tana son kara raya dangantakar abokantaka a tsakaninta da kungiyar AU, da kara yin mu'amala kan manyan manufofin samun bunkasuwa, da sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu da samun ci gaba tare.
A nasa bangare, Faki ya nuna godiya ga kasar Sin bisa ga goyon baya da take nunawa ga sha'anin samun bunkasuwar nahiyar cikin lumana da kuma raya kungiyar AU. Kana kungiyar AU tana son hada kai tare da kasar Sin wajen ganin an samu nasarar shirya taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da za a yi a birnin Beijing a bana. (Zainab)