A yayin taron, jami'an 2 sun tattauna yadda za su zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, sa'an nan sun tabbatar da fannoni 5 da za su yi kokarin gudanar da hadin gwiwa. A cewar mista Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin, wadannan fannoni 5 sun hada da, kara karfin kungiyar AU na daidaita al'amura, da kara gina kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afirka, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka, da raya harkokin kula da lafiyar jikin jama'a da jinyar wadanda suka kamuwa da cututtuka a Afirka, gami da karfafa hadin gwiwa a fannin yawon shakatawa da zirga-zirgar jiragen sama.
A cewar jami'in kasar Sin, hadin gwiwa a wadannan fannoni sun shafi daukacin nahiyar Afirka, zai kuma kyautata huldar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar ta AU.(Bello Wang)