in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar zartarwar AU zai kawo ziyara kasar Sin
2018-02-05 19:52:21 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya sanar a yau Litinin cewa, shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka(AU) Moussa Faki Mahamat zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 7 zuwa 9 ga wannan wata bisa gayyatar ministan harkokin wajen Sin Wang Yi.

A lokacin wannan ziyara wadda ita ce ta farko da zai kawo kasar ta Sin, an sa ran Moussa Faki Mahamat da Wang Yi za su jagoranci tattaunawar Sin da AU bisa manyan tsare-tsare karo na 7 tare, inda jami'an biyu za su yi musayar ra'ayoyi game da batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake shafarsu.

Mr. Geng ya kuma yabawa kungiyar ta AU a matsayin daya daga cikin muhimman kungiyoyin dake wakiltar gwamnatoci a Afirka. Yana mai cewa, har kullum kasar Sin tana karfafa alaka da kungiyar daga manyan tsare-tsare zuwa kyakkyawar makoma ta dogon lokaci.

Ya kuma bayyana fatan cewa, ziyarar za ta kara bunkasa amincewa da juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannoni daban-daban, tare kuma da karfafa dangantakar dake tsakanin sassan biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China