in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faki ya karyata rahoton da ke zargin Sin da yiwa AU leken asiri
2018-02-08 19:15:04 cri

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka(AU) Moussa Faki Mahamat ya ce zargin da ake yiwa kasar Sin wai tana yiwa kungiyar ta AU leken asiri, karya ce tsagwaronta.

Faki ya bayyana haka ne yau Alhamis a nan birnin Beijing, yayin da yake jawabi a taron tattaunawa bisa manya tsare-tsare tsakanin Sin da AU karo na 7 da suka jagoranta shi da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi.

Ya ce, babu abin da zai raunana dangantakar dake tsakanin Sin da AU, kuma irin wadannan rahotanni ba za su lalata dangantakar dake tsakaninsu ba.

Faki ya ce kungiyar AU kungiya ce ta kasa da kasa ba hukumar tsaro mai muhimman bayanan sirri ba, a don haka ko kadan kasar Sin ba za ta yiwa kungiyar wani leken asiri ba saboda kyakkyawar alakar dake tsakanin sassan biyu.

Jami'in na AU ya ce a shirye kungiyar take ta kara hada kai da kasar Sin ta yadda al'ummomin nahiyar za su amfana, kuma irin wadannan labaran kanzon kurege ba za su dauke musu hankali ba.

Wannan ita ce ziyarar Faki ta farko da ya kawo kasar Sin tun bayan da ya kama aiki a watan Maris din shekarar 2017 da ta gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China