in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IOC: 'yan wasan guje-guje 13 ne za su wakilci Afirka a gasar Olympics da za a yi a PyeongChang
2018-02-09 19:07:14 cri

Kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya (OIC) ya tabbatar da cewa, 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle 13 ne daga nahiyar Afirka za su halarci gasar wasannin Olympics ta lokacin huturu da aka bude yau a PyeongChang na kasar Koriya ta kudu.

A cikin wannan adadi, kasashen Afirka guda 8 ne za su shiga gasar, adadi mafi yawa daga nahiyar a tarihin gasar Olympics ta lokacin hunturu.

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasar Kenya Paul Tergat ya ce, akwai alamun 'yar wasan zamiyar kankara dake wakiltar kasar Sabrina Wanjikuza tana iya lashe lambar yabo a gasar ta bana. Su ma kasashen Najeriya da Eritrea za su shiga wannan gasa, sauran sun hada da Afirka ta kudu da Ghana, da Morocco da Madagascar da kuma Togo.

Kasashe da yankuna 92 ne ake sa ran za su fafata a wasannin 2,925 a gasar ta bana, wadda ake ganin ita ce gasar da ta samu halarcin 'yan wasa a tarihi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China