in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Afrika ta ayyana kasashe 3 da za su maye gurbin Kenya
2017-10-03 13:33:48 cri

Jiya Litinin, hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta Afrika (CAF), ta tabbatar da cewar, kasashen Equatorial Guinea, Habasha da Morocco, su ne ake sa ran za su maye gurbin kasar Kenya na karbar bakuncin gasar wasannin cin kofin kasashen nahiyar Afrika ta CHAN ta shekarar 2018.

An yanke shewarar kwace ikon karbar bakuncin wasan daga hannun kasar Kenya ne a ranar 23 ga watan Satumba, a lokacin babban taron da aka gudanar na CAF a Accra, na kasar Ghana, duk kuwa da nasarar da kasar ta samu na karbar bakuncin wasan  wanda aka tallata a shekarar 2014, , saboda kasar ta gaza cika ka'idojin da aka tsara wandada suka shafi rashin ingancin filin wasanta.

Tuni dai aka tallata neman kasar da za ta iya karbar bakuncin gasar ta ranar 30 ga watan nan na Oktoba, yayin da kasashen uku suka nuna sha'awarsu.

Shugaban hukumar ta CAF Ahmad Ahmad, ya ayyana kasar ta Kenya da cewar ba ta cancanci karbar bakuncin gasar ba, sakamakon rashin ingancin kayayyakin aiki a filin wasan kasar, da kuma rashin gaskiyar da bangaren jagororin hukumar wasannin kasar Kenyan suka nuna, da kuma matsalar dambarwar siyasar dake neman hargitsa al'amura a kasar. Kasar Kenya ta ayyana ranar 26 ga wannan wata, a matsayin ranar da za ta sake gudanar da zaben shugaban kasar a karo na biyu.

Da ma dai tuni dukkannin tawagogin wasannin kwallon kafa na kasashe 15 suka amince da wannan kuduri. Wadanda suka hada da kasashen Burkina Faso, Guinea, Jamhuriyar Congo, Libya, Morocco, Kamaru, Nijeriya, Zambiya, Uganda, Angola, Ekwatoriyal Guinea, Mauritaniya, Sudan, Cote d'Ivoire da Namibiya.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China