in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta karbi bakuncin taron hukumar shirya gasar cin kofin tsalle-tsalle na Afrika karo na 27
2017-10-10 09:59:32 cri
Hukumomin kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Afrika, sun tattauna a jiya Litinin, kan makomar 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle yayin taron hukumar shirya gasar cin kofin wasannin tsalle-tsalle na Afrika karo na 27 da ya gudana a birnin Skhirat na Morocco.

Sarkin Morocco Muhammad VI ya shaidawa taron cewa, a galibin wasanni, 'yan wasan Afrika sun fi na ko ina a duniya, inda suke kara burgewa da sabbin nasarori da kwazo.

Sarkin ya ce duk da haka, bai kamata wadannan nasarori su hana ganin gaskiyar al'amari ba, yana mai cewa filayen wasannin a kasashen Afrika na cikin mawuyacin hali.

Ya ce za a iya shawo kan wannan matsala ne kadai, idan aka dauki tartibiyar dabara da za ta dace da yanayin wasannin a fadin duniya.

Ya ce dole ne dabarar ta kasance bisa kyakkyawan kudurin shugabanci da inganta kwarewar 'yan wasa tare da ba su horo bisa tsari na zamani da samar da kayayyakin wasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China