in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi gargadi game da mike kafa a yaki da IS
2018-02-09 10:48:26 cri

Wani babban jami'in MDD ya yi gargadi game da mike kafa a yakin da ake yi da mayakan masu da'awar kafa daular musulunci IS, duk kuwa da irin koma bayan da dakarun mayakan na IS suka samu a 'yan kwanakin nan a kasashen Iraqi, Syria da kudancin Philippines.

A halin yanzu, yakin da ake yi da kungiyar IS ya shiga wani sabon mataki, bayan da aka samu gagarumar galaba a kansu, amma duk da haka kungiyar da sauran kawayenta na ci gaba da zama babbar barazana ga kasashen duniya, kamar yadda Vladimir Voronkov, jami'in sashen yaki da ta'addanci na MDD ya bayyanawa kwamitin sulhun MDDr.

A halin yanzu, mayakan na IS ba su mai da hankali wajen kwace wasu yankuna. A maimakon hakan, su fi mayar da hankali ne wajen neman goyon bayan kananan kungiyoyi da daidakun jama'a don su mara musu baya, inda hakan zai ba su damar kaddamar da hare hare, in ji Vrononkov.

Ko da yake, abu ne mai matukar wahala a iya tantance adadin mayakan kungiyar 'yan ta'addan da suka rage a kasashen Iraqi da Syria, amma yadda mayakan ke kwarara zuwa kasashen ya kusa zuwa karshe. Sai dai kuma, dawowar mayakan 'yan ta'addan na kasashen waje, da kuma bazuwar wasu zuwa sauran sassa na duniya na ci gaba da zama a matsayin babbar barazana ga sha'anin tsaron kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China