in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taron MDD zai kira zaman gaggawa game da birnin Kudus
2017-12-20 15:01:39 cri

Wata majiya daga MDD na cewa, a gobe Alhamis ne ake sa ran babban zauren MDDr zai kira wani taron gaggawa, bayan da Amurka ta hau kujerar naki kan kudurin da kasar Masar ta gabatar game da matakin Amurka na ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.

Wakilin Palasdinu dake MDD Riyad Mansour ya ce, yana fatan babban taron MDDr zai kada kuri'ar amincewa da daftarin da zai bukaci shugaba Trump na Amurka ya janye matakin da ya dauka game da birnin Kudus.

Majiyar ta kara da cewa, ba safai babban taron ya ke ganawar gaggawa ba, kuma taron na gobe Alhamis ci gaba ne kan wanda ya gabata game da wannan batu.

Wakilin na Palasdfinu da sauran jami'ai daga kasashen Larabawa sun gana da shugaban babban taron MDD na wannan karo Miroslav Lajcak, bayan da Amurka ta hau kujerar naki a kan kuduri. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China