in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci Isra'ila ta mayar da filayen da ta kwace a yammacin kogin Jordan
2016-03-16 10:38:08 cri

Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, ya bukaci gwamnatin Isra'ila da ta mayar da filayen da ta mamaye a yankunan yammacin kogin Jordan, Ban ya bayyana abin da Isra'ilan ke yi a matsayin dalilan dake kawo cikas wajen warware takaddamar dake tsakaninta da al'ummar Palastinawa.

Mai magana da yawun sakatare janar na MDD Stephane Dujarric ya ce, Ban ya fada cewar, matakin Isra'ilan na kwace matsugunann Palastinawa kimanin muraba'in kilomita 2,340 a kwanan nan, na daga cikin dalilan dake hana ruwa gudu game da warware rikicin dake wanzuwa tsakanin bangarorun biyu.

Mista Ban ya bukaci gwamnatiin Isra'ilar da ta gaggauta mayar da yankunan Palastinawa da ta mamaye ba bisa ka'ida ba, domin samun dawwamamman zaman lafiya da kawo karshen takun sakar dake tsakanin bangarorin biyu.

Rikicin bangarorin biyu wanda ke samun goyon bayan kasashen duniya da dama, za'a kawo karshen sa ne, ta hanyar samar da yantacciyar kasa mai cin gashin kanta ga al'ummar Palastinawa, da kuma mayar musu da gidajensu wadanda Yahudawan Isra'ila suka mamaye a yankunan yamma da kogin Jordan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China