in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya goyi bayan kudurin katse hanyoyi da IS ke samun kudadenta
2015-12-18 10:08:22 cri

A jiya Alhamis ne kwamitin sulhu na MDD ya amince bai daya da wani kuduri da ke bukatar katse duk wasu kafofin da kungiyar IS ke samun kudadenta, a wani mataki da kasashen duniya ke dauka na yaki da ayyukan ta'addanci.

Sauran matakan da kwamitin ya amince da su kan kungiyar ta IS sun hada da kwace kadarori, haramta yin tafiye-tafiya da kuma hana sayarwa kungiyar da ake kira ISIL da kuma Daesh makamai.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka kungiyar na rike da wurare da dama na kasashen Syria da Iraki, ciki har da filayen mai da iskar gas

Kudurin ya kuma lura da cewa, kungiyar ISIL da ke da alaka da kungiyar al-Qaida, wata babbar barazana ce ga harkokin tsaro a duniya baki daya. A saboda haka, kudurin ya ce, hanya guda ta kawar da wannan kungiya ita ce, kungiyoyi na kasa da kasa da na shiya-shiya da daukacin kasashen duniya su hada kai bisa dokokin kasa da kasa da ka'idojin MDD.

A jawabinsa gabanin amincewa da wannan kuduri, babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya ce, kungiyar Daesh da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda suna watsa munanan ikidunsu tare da kai hare-hare kan fararen hula. Don haka wajibi ne a tashi tsaye don ganin an toshe dukkan kafofin da suke samu kudaden su kafin su kara yin illa ga al'umma.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China