in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta kaddamar da shirin tallafawa mata da aka ci zarafinsu
2017-12-05 10:19:06 cri

Kasar Zambia ta kaddamar da wani shiri na taimakawa mata da suka fuskanci cin zarafi da musgunawa.

Shirin na samar da kudin shiga ga wadanda aka ci zarafinsu da aka kaddamar jiya da hadin gwiwar hukumar kwadago ta duniya ILO, zai taimaka wajen adana rahoton dukkan wadanda suka tsira daga cin zarafi ko musgunawa, domin taimaka musu da hanyoyin samun kudin shiga.

Yayin kaddamar da shirin, babban sakataren ma'aikatar kula da jinsi ta Zambia Felix Phiri, ya ce an kirkiro shirin ne saboda karuwar rahotannin cin zarafi, wanda ya zama abun damuwa ga gwamnati.

A cewarsa, shirin zai taimakawa mata da suka tsira daga matsalar da hanyoyin samun kudin shiga, domin sakamakon bincike ya nuna talauci na daya daga cikin abubuwa dake haddasa cin zarafi da musgunawa.

Felix Phiri, ya kuma bukaci wadanda ake cin zarafinsu da su rika kai rahoto ga hukumomin da suka dace, yana mai cewa, gaza yin hakan ne ya sa matsalar ta yi kamari.

Zambia na fuskantar karuwar matsalar cin zarafi da musgunawa mata, domin abu ne mawuyaci a shafe mako guda ba tare da an samu rahoton matsalar daga kafafen yada labaran kasar ba.

Gwamnatin kasar ta kaddamar da wani gangamin kwanaki 16 a watan da ya gabata, domin nuna adawa da cin zarafi da musgunawa mata, inda aka masa taken "kada a bar kowa a baya, a kawo karhen musgunawa mata yanzu."

Gangami ne na duniya domin kalubalantar cin zarafi da musgunawa mata da 'yan mata, inda yake gudana tun daga ranar 25 ga watan Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China