in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin kasasehn Afrika sun kaddamar da wani shiri da zai shigar da mata bangaren makamashi
2017-12-04 10:19:23 cri
Ministocin kasashen Afrika sun kaddamar da wani shirin dake da nufin shigar da mata kai tsaye cikin harkokin bangaren makamashi.

Shirin karfafawa matan Afrika 'yan kasuwa shiga harkokin makamashi da taron ministocin Afrika kan muhalli ya kaddamar jiya Lahadi a birnin Nairobi, na da nufin kyautata kudurin shugabanci daga gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki, ta yadda za a samu jarin da zai magance matsalolin da suka shafi samun makamashi mai tsafta da rahusa.

A cewar sakatariyar gwamnatin kasar Kenya mai kula da muhalli da albarkatu Judi Wakhungu, fito da rawar da mata za su iya takawa a fannin samar da makamashi mai tsafta na da muhimmanci ga cimma manufofin ci gaba masu dorewa da dama da kuma burin samar da ci gaba ta bai daya a nahiyar Afrika kawo shekarar 2063.

Judi Wakhungu ta ce taron ministocin zai samar da goyon bayan da ake bukata ga shirin, tana mai bukatar sauran masu ruwa da tsaki su shiga a dama da su.

A cewar MDD, sama da mutane miliyan 600 dake nahiyar ne ba sa samun lantarki, yayin da sama da 600,000, kaso 60 daga cikinsu mata, ke mutuwa sakamakon gurbatar iska daga kayayyakin amfani na gida. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China